Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci da Sudan da Sudan ta Kudu su dau matakan kaucewa yaki, a yayin da bangarorin biyu ke fara wani sabon zagayen tattaunawa a kasar Habasha.
Bangarorin Sudan din biyu na mummunar takaddama kan mai, suna kuma zargin juna da mara wa ‘yan tawayen juna.
Jakada Mark Lyall Grant na Burtaniya, wanda ke rike da mukamin na karba-karba na kwamitin, ya fadi yau Talata cewa Kwamitin na cikin matukar damuwa game da rahotannin girke dakaru da kuma yawan kai hare-haren jirgin sama a kan iyakoki.
Ya yi kira ga kasashen da su mutunta yarjajjeniyar daukar matakan lumanar da su ka rattaba hannu a kai wata guda da ya gabata.
“Kwamitin Tsaron na bukatar kowane bangare ya kwance damarar yaki a kusa da kan iyakoki ya kuma kawo karshen yawan tashe-tashen hankula.” In ji shi
Kwamitin na kuma bukatar Sudan da Sudan ta Kudu da kar kowannensu ya dau wani matakin da zai yi illa ga matakan tsaro da kuma kwanciyar hankalin dan’uwansa.
Shawarar ta zo ne a daidai lokacin da Sudan da Sudan ta Kudu su ka fara tattaunawar kwanaki 10 kamar yadda aka tsara a birnin Addis Ababa. Kungiyar Tarayyar Afirka na kokarin shiga tsakani game da takaddamar raba dukiyar mai, da kan iyakar da ba a shata ba da kuma batun kasancewa dan kasa wadanda duk batutuwa ne da su ka taso bayan samun ‘yancin kan Sudan a cikin watan Yuni.