Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadan kabilanci Ya Kashe Mutane Akalla 100 A Sudan ta Kudu

Wata mace 'yar kabilar Murle tana jiran agajin abinci a garin Pibor. An dauki hoton ne ranar 2 Fabrairu 2012.
Wata mace 'yar kabilar Murle tana jiran agajin abinci a garin Pibor. An dauki hoton ne ranar 2 Fabrairu 2012.

Jami’ai a Sudan ta Kudu sun ce an kashe mutane akalla 100, a yayin da wasu daruruwan suka ji rauni a sabon fadan kabilancin da ya barke a kasar.

Jami’ai a Sudan ta Kudu sun ce an kashe mutane akalla 100, a yayin da wasu daruruwan suka ji rauni a sabon fadan kabilancin da ya barke a kasar.

Gwamnan Jihar Jonglei, inda ake wannan rikicin, Kuol Manyang, ya fadawa taron ‘yan jarida yau litinin cewa matasan kabilar Murle a karamar hukumar Akobo sune suka kai farmaki suka kashe ‘yan kabilar Lou Nuer, suka raba mutane fiye da dubu 10 da gidajensu, sannan aka sace dubban shanu.

Kwamishina mai kula da karamar hukumar Akobo, Pal Mai, yace an fara fada ranar asabar, aka kuma kwashi tsawon ranar ana kazamin ba ta kashi.

A cikin ‘yan shekarun nan, ‘yan kabilar Murle da Lou Nuer su na kai munanan hare-hare masu alaka da satar shanu a kan junansu.

Hari na baya-bayan nan ya wakana a ranar jajiberen wani shirin kwance damarar yaki da aka shirya da nufin sassauto da tankiya a Jihar Jonglei.

Wannan fada yana gurgunta kokarin kawo tsaro da kwanciyar hankali ga Sudan ta Kudu, wadda ita ce ‘yar auta daga cikin kasashen duniya.

XS
SM
MD
LG