Majalisar Dinkin Duniya Ta Baiyyana Aikinta Bisan Lafiyar Kananan Yara

Ban Ki-moon

Sakataren kungiyara majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon yace za’a sa kokari wajen inganta lafiyar mata da yara tawurin wani sabon shiri wanda za’a raba ra’ayoyi da nasarori cikin kasashe masu tasowa.
Sakataren kungiyara majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon yace za’a sa kokari wajen inganta lafiyar mata da yara tawurin wani sabon shiri wanda za’a raba ra’ayoyi da nasarori cikin kasashe masu tasowa.

Ban Ki-moon a jihar New York, tare da mambobin hadin gwuiwa da yawan jama’a da cigaba suka hadu a wani lokacin cin abinci domin su tattauna aiyyukan da kudu – kudu zasuyi na hada hannu wajen inganta lafiyar mata da yara da kuma dukan abinda ya shafi lafiya na cigaban wannan karni.

Wani bayanin majalisar dinkin duniya da aka bayar a New York a ranar Talata, Ban yace “hadin hannun ‘yan kudu-kudu yafi hadin kan kasuwanci; yana kan rarraba sani ne, iyawa da kuma gwaninta. Shine farkon tushen hadin kan dukan duniya domin yin aiki.”

Yace wannan sabon mika kai ga shirin Sakataren Majalisar dinkin duniya na cigaban kowacce mace da kuma kowanne yaro zai tabbatar da shirinta da aiyyukanta zasu inganta hadin mata da yara a matsayin masu amfana daga dukan shirye shirye da kokarinsu.

Shugaban majalisar dinkin duniya yace zasu cinma wannan ne tawurin yada ilimi, koyarda aiyyukan hannu, aika da kayayyaki da kuma iyawa tawurin bada shawarwari da tattaunawa bisan ka’idoji, hada hannu da kuma neman kayan aiki, ma’amala tsakanin kasashen duniya da kuma bincike.

“Kowacce mace da kowanne yaro wani aiki ne da yake bisan sakataren majalisar dinkin duniya domin ya jawo hankalin mutane da kuma ya karfafa aikin duniya na inganta lafiyar mata da yara a kewayen duniya baki daya.’’

Aikin PPD zai taimaka karfafa hada aiyyuka daga mambobinsu 26 bisan mahimman taimako kan mata da yara.

Mr. GhulamNabi Azad, shugaban PPD da kuma ministan lafiya na Indiya da kuma halin lafiya na iyalai, yace, “PPD ta mika kai wajen jawo hankalin taimakon siyasa da kuma kokarin neman kayan taimako daga mambobin jihohi na majalisar dinkin Duniya.

PPD wata kungiyar hadin hannun gwamnati ce wadda ta hada kasashe masu tasowa 26.

Tana da hanyoyin inganta hadin hannu da hada kai tsakanin kasashen dake mambobi, zuwaga cinma manufofin taron dukan duniya na yawan jama’a da kuma cigaba, shirin aiyyuka da kuma shirye shiryen gina kasa na MDGs.