Wani jami'in ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Guinea, mai suna Sokoba Keita ya gayawa sashen Faransancin Muryar Amurka ranar asabar cewa an tabbatar da cewa daga cikin samfurin kwayoyin cuta 12 da aka tura kasar Faransa 3 na cutar Ebola ne.
Likitoci sun samu mutane 48 da suka kamu da cutar daga lokacin da aka bada rahoton barkewar ta a watan jiya. Sun ce haka kuma an samu wasu mutane uku a Conakry babban birnin kasar, wadanda ake jin cewa cutar ce ta kama su.
Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Guinea ta ce jami'an Hukumar Lafiya ta Duniya za su isa kasar ranar Lahadi domin su yi karin gwaje-gwaje a inda aka samu bullar cutar.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ce haka kuma, akwai damuwa da fargabar cewa watakila cutar ta Ebola da ta barke a kasar Guinea ta bazu zuwa makwafciyar kasar Saliyo.
Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ko OMS, ta ce cutar Ebola na cikin cututtuka mafiya tsananin lahanin da aka sani.
Ana daukan cutar ce ta hanyar yin ma'amala ta kai tsaye da najasar wanda ya kamu da ita, ko kuma a taba jikin wanda ya kamu da ita. Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce haka kuma ana iya kamuwa da cutar ta hanyar yin ma'amala ta kai tsaye da dabbobin da suka kamu da ita, har ma da mushen su.