Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin, ya kada kur’ar amincewa da girke dakarun kiyaye zaman lafiya wajen 4,200 da gagarimin rinjaye, na tsawon watanni 6 a yankin Abyei na kasar Sudan da ake takaddama a kai.
Kasar Habasha ta amince ta samar da sojojin.
Kudurin, wanda Kwamitin Tsaron ya cimma a jiya Litini na kuma neman da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya tabbatar cewa an sa ido sosai kan batun hakkin dan adam a yankin na Abyei.
Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton ta fadi a wani jawabinta cewa Amurka ta yaba da amincewa da kudurin da aka yi ba tare da bata lokaci ba. Ta bayyana batun girke sojojin da cewa mataki ne mai muhimmanci na aiwatar da yarjajjeniyar da aka cimma tsakanin Kudu da arewacin Sudan a makon jiya kan janye mayaka daga yankin na Abyei da kuma girke dakarun tabbatar da zaman lafiya.