Majalisar Dattijai Zata ci Gaba Muhawara Kan Tsawaita Dokar ta Baci

Shugaba Goodluck Jonathan.

A yau ma majalisar dattijan tayi zamanta ne cikin sirri, kuma wakilan sunki suyi magana bayan da suka fito.

A zaman da majalisar dattijan Najeriya tayi ranar talata, ta tashi ba tareda ta amince da bukatar da shugaba Goodluck Jonathan ya gabatar mata na neman sabunta dokar ta baci da gwamnatin ta kafa a jihohi uku da suke arewa maso gabashin kasar; sune Barno, Yobe da kuma Adamawa.

A tattaunawar da Bello Galadanci yayi da yayi da wakiliyar Sashen Hausa Madina Dauda a Abuja, Madina tace, daya daga cikin abunda yake janyo cikas kan wannan batu shine a cikin wannan sabuwar wasikar, shugaba Goodluck Jonathan baiyi bayanan da ya saba yi a wasikun da ya rubutawa majalisar dattijai kan wannan batun na dokar ta baci ba.

Misali, a baya cikin wasikun, shugaban kasa yana bayani kan tsawon dokar ta bacin, da batun wadda za'a azawa nauyin alhakin biyan sojoji hakkinsu, amma a wannan karon baiyi haka.

Rashin wannan bayanin yasa aka fara rade raden watakil shugaban kasan yana so ne ya nada kantomomi a madadin gwamnonin da suke mulki a wadannan jihohi.

Wannan yana daga cikin dalilai da suka sa ake jin wadansu wakilai musamman 'yan hamayya suke turjiya kan sabunta wannan dokar ta bacin.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattijai Zata ci Gaba Muhawara Kan Tsawaita Dokar ta Baci