Wasu sun fadi albarkacin bakinsu dangane da amincewa da nadin Ibrahim Shekarau da majalisar dattawa tayi ya zama minista a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan.
Wani yace yana ganin nadin nasa cigaba ne idan zai tsaya yayi aiki tsakaninsa da Allah ya cire batun siyasa. Nadin Kano aka yiwa. Wani kuma cewa yayi nadin Ibrahim Shekarau ya nuna cewa 'yan siyasan Najeriya ba domin talaka su keyi ba, domin kansu ne. Suna canza sheka ne kawai domin cimma muradun kansu. Ibrahim Shekarau ya canza sheka ne domin ya samu mukami gashi kuma ya samu.
Amma wani yana ganin babban alheri ne ya samu jihar Kano. Yace ya tabbata Ibrahim Shekarau mutum ne gogaggye wanda zai iya kawo duk cigaban da ake bukata. Wani kuma yana fatan za'a bashi wurin aikin da ya kware akai wato ma'aikatar ilimi domin ya kawo karshen tabarbarewar ilimin firamare.
Yanzu jihar Kano nada kujerun ministoci guda biyu ke nan a tarayyar Najeriya. Alhaji Musa Dan Birni jigo a jam'iyyar PDP reshen Kano yace abun da ya faru alheri ne yake haskawa domin Ibrahim Shekarau albarka ne ga jam'iyyar. PDP zata cigaba da habaka a Kano.
Umar Labaran Danga wani na hannun daman gwamnan Kano yace a wurinsu nadin babu wani kalubale dake fuskantarsu game da nada Ibrahim Shekarau minista. Yace abun da gwamna Rabiu Kwankwaso yayi a Kano babu wani dan siyasa mai neman kudi da zai iya yi. Gwamna Kwankwaso kalubale ne ga wanda ya nada Ibrahim Shekarau.
Wasu ma na ganin karin minista a jihar Kano ba zai yi wani tasiri ba a zaben shekarar 2015.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5