'Yan majalisar dattawan Najeriya sun yi muhawara mai susa zuciya akan shirin gwamnatin jihar Imo na neman duk wani dan asalin arewacin Najeriya da yayi ragista da kudi nera dubu kafin a bari ya cigaba da zama a jihar.
Tsarin na gwqamnatin Imo yace duk wani bako musamman daga jihohin arewa da yake da niyyar shiga jihar Imo sai an tantanceshi kana a bashi wata takardar shaida bayan yayi ragistar takardar akan kudi nera dubu daya. Wannan abun Babayo Gamawa yace ba daidai ba ne.
Babayo Gamawa yace Najeriya ba shagon wani ba ne. Najeriya kuma ba kamfanin wani ba ne. Idan 'yan kudu suka ce zasu musgunawa mutanen arewa to suma za'a musgunawa nasu mutanen dake arewa kuma su ne zasu fi kowa shan wahala. Yace ba'a fata cewa za'a kai wani matsayi da za'a ce wani ba zai shiga jefen wani ba. Yace ana fata abun da aka kirkiro a jihar Imo ba zai yi tasiri ba.
Kashi arba'in da daya da kashi arba'in da biyu na kundun tsarin mulkin kasar Najeriya ya ba kowane dan kasa 'yancin zama a kowane sashi na kasar ba tare da wata tsamgwama ba.
Sanata Alkali Jajere yace an yi kakkausar magana a majalisa domin a ja kunnen gwamnan Imo ya bar mugun kudurin da ya dauko. Bugu da kari sun gayawa gwamnatin tarayya ta fadawa duk jami'an tsaronta dake jihar Imo kada su bashi goyon baya ko hadin kai domin gabatar da dokar. Shi ma gwamnan majalisa ta ja kunnensa da ya janye dokar ba tare da bata lokaci ba.
Idan ba'a manta ba kwana kwanan nan aka kama 'yan arewa 'yan cirani su 486 a jihar Abia ana zarginsu da cewa 'yan kungiyar Boko Harama ne.
Ga rahoton Medina Dauda.