Bayan da shugaban majalisar dattawan Najeriya Sanata Bukola Saraki ya sanarda majalisar cewa shugaban kasa ya cire sunan Alhaji Ahmed Isa Ibeto daga sunayen wadanda ya nemi majalisar ta tantance, 'yan majalisar sun amince da 18 daga cikin 21 na farko dake gabansu.
Wanda shugaba Buhari ya cire wato Alhaji Ahmed Isa Ibeto shi ne tsohon mataimakin gwamnan jihar a karkashin jam'iyyar PDP. Amma shugaban bai bada hujjar cire sunan ba. Shi da gwamnan jihar da sakataren gwamnatin jihar dukansu daga yanki daya suka fito.
Cikin mutane 18 da majalisar ta amince dasu akwai wasu da mutane da dama da suka kawo korafe korafe a kansu.
Imrana Wada shugaban kungiyar habbaka matasan arewa yace duk lokacin da ake son a dauki mutane biyar kamata ya yi akwai matasa biyu domin duk fafutikar da aka yi wurin zaben shugaba Buhari matasa ne suka yi. Kasar Najeriya matasa suka sa gaba saboda su ne zasu gajeta. Su ne da sauran lokaci.
Imrana yace matasa yakamata a jagorantas domin su yiwa na bayansu jagoranci. Yace to amma tsoffi shugaba Buhari ya kawo ya nada ministoci. Inji Imrana akwai wanda ya yi minista lokacin gwamnatin Shagari yanzu kuma an dawo dashi a matsayin minista.
Su ma 'yan asalin yankin birnin tarayya suna gani ba'a yi dasu ba saboda ba'a basu mukamin minista ko daya ba.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5