John Ratcliff Ya Zama Shugaban Hukumar Leken Asirin Amurka CIA.

John Ratcliffe sworn in as the CIA Director, in Washington

Ratcliffe ya bayyana cewa zai kawo sauye sauye, sannan ya kara da cewa hukumar liken asirin zata mai da hankalin wajen tattara bayanan mutane da kuma mai da martini kan masu adawa da Amurka.

Mahukuntan Amurka sun tabbatar da mutum na biyu a rukunin mutane masu mahimmanci da zasu yi aiki tare da tawagar tsaron kasar Trump jiya Alkhamis, kuri’u 74-25 da ya kai Ratcliffe ga nasarar zama Darektan hukumar leken asirin kasar na 25.

Ratcliffe, wanda ya taba rike mukamin Darekta a hukumar tattara bayanan kasa a karshen wa’adin Trump na farko, ya sha rantsuwar kama aiki sa’o’I 2 bayan tabbatar da shi akan wannan matsayi, yayin da mataimakin shugaban kasa J.D. Vance ya jagoranci rantsar da shi.

Vance ya ayyana Ratcliffe da “Babban mai kishin kasa” sannan ya ce shi amintacen shugaban kasa ne.

Yanzu Ratcliffe zai jagoranci wani aikin tattara bayanan sirrin da Trump da ‘yan Republican suka yi sukar lamirin faruwar wasu abubuwa a wurare irin su Ukraine, Afghanistan, da gabas ta tsakiya, da kuma yadda aka yi amfani da bayanan sirrin da hukumar ta tattara don kare dokokin gwamnatin da ta shude.

A yayin da majalisa tayi zaman tantance shi a makon jiya, Ratcliffe ya bayyana cewa zai kawo wasu sauye sauye, sannan ya kara da cewa hukumar leken asirin, zata mai da hankalin wajen tattara bayanan mutane da kuma mai da martini kan masu adawa da Amurka.