Majalisar Dattawan Najeriya Ta Tabbatar Da Sunayen Ministoci 45 Daga Cikin 48

Shugaba Tinubu

Tabbatar da hakan ya biyo bayan nazari da amincewa da wadanda aka nada a wani zama mafi tsawo da majalisar ta yi a cikin wattani biyu da aka kaddamar da ita.

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da MInistoci 45 cikin 48 din da ta kwashe tsawon kwanaki takwas tana tantance su.

Majalisar ta amince da tsofaffin Gwamnoni 4 ciki har da tsohon Gwamnan jihar Ribas Nyesome Wike da tsohon Gamnan Jihar Zamfara Bello Mattawalle, da na Jihar Osun Gboyega Oyetola, da Mohammadu Badaru na jihar Jigawa.

Hakazalika, majalisar ta amince da Ibrahim Geidam na jihar Yobe, amma ta dage tabbatar da sunayen mutane uku, da tsohon Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa'i da tsohon Sanata daga jihar Taraba Sani Danladi, da kuma 'yar jihar Delta Madam Stella Okotete.

Sanata mai wakiltar jihar Filato ta tsakiya Diket Plang ya bayana dalilin haka, ya ce mutane uku da ba'a tabbatar da su ba suna jiran tabbaci ne daga hukumar tsaro.

Diket ya ce Majalisar za ta amince da bayanan zaman tantance sunayen ministocin kafin a kai wa Shugaban kasa shi ma ya amince sannan a nada su a mukaman su.

Shugaba Tinubu ya mika sunayen wadanda aka nada ne a wasu wasiku guda uku daban daban ga Majalisar a ranakun 28 ga watan Yuli, sai kuma ranakun 3 da 4 ga wannan wata na Agusta.

A cikin wasikarsa ta 4 ga watan Agusta ne shugaban ya sanar da Majalisar cewa ya janye daya daga cikin wadanda aka nada daga kano Maryam Shetty sannan ya maye gurbinta da Mariya Mahmud Bunkure.

Sanata mai wakiltan Jihar Bauchi ta Kudu Shehu Buba Umar ya ce yawan Ministoci da Shugaban kasa ya ke so ya nada, alamu ne na ci gaba, inda yace kundin tsarin mulki ya ba da dama a nada Ministoci 37 idan an hada da Birnin Taraiyya, sannan ba'a haramta wa shugaban kasa ya yi kari ba, inda ya ce jihar sa ta Bauchi ta samu Ministoci biyu, kuma akwai jihohi haka da dama. Shehu ya ce siyasa haka ta gada.

Amma Kwararre a fanin siyasa kuma Malami a jami'ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi tsokaci ne akan batun cancantar wadanda aka tantance su domin zama Ministoci inda ya ce wadanda aka zabo domin zama ministoci, da wadanda suka zabo su, babu wani batu na ci gaban kasa ko kishin kasa a gaban su, kawai an zabo su domin a saka masu wata rawa da suka taka ko a lokacin zabe ko kuma kyautata wa siyasar nan gaba, ko kuma kawai a ce ku je kuma ku samu na magance talauci.

Bayan kammala aikin tantance ministocin, sai majalisar dattawa ta nada kwamitoci wadanda za su gudanar da aiyukan cigaban kasa 73.

Majalisar ta fara hutu a yau din nan har zuwa ranar 26 ga watan satumba.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Sunayen Ministoci 45 Daga Cikin 48 Da Tinubu Ya Mika Mata.