Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Matasa Suka Nuna Rashin Jin Dadi Kan Cire Sunan Maryam Shetty A Sunayen Ministoci


Maryam Shetty
Maryam Shetty

"Wannan labari a gaskiya bai mana dadi ba, saboda, ya kashe mana kwarin gwiwa da kuma mafarkin da muke da shi na cewa mu ma za mu iya kasancewa wani abu ba tare da an duba karancin shekarunmu ba." In ji Zainab Alkali.

Matasa na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu, da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dauka na cire sunan Maryam Shetty daga jerin ministocin da ya mikawa Majalisar Dattawa.

Kwana biyu da aike sunayen, kwatsam Tinubu ya cire sunan Shetty, matashiya daya kacal daga arewacin kasar.

Har zuwa lokacin hada wannan labari, fadar shugaban kasar ba ta yi bayani kan daukan wannan mataki ba.

Sai dai sauran matasan da suka fito daga kudancin kasar, sun kai bantensu.

Hakan ya sa ake ganin kamar wani ma tattare da matsin lamba na masu ruwa da tsaki daga arewacin kasar, kuma cin fuska ne ga matasa a cewar Komred Kabir, Dakata, babban daraktan cibiyar wayar da kan al'umma kan shugabanci nagari da kuma tabbatar da adalci (KAJA.)

Cire sunan dai ya bar baya da kura, inda matasa da dama suka nuna rashin jin dadinsu, saboda suna tunanin gwamnatin ta Tinubu za ta dama dasu, sai ga shi ba'a je ko ina ba anfara tsince sunayensu.

Adnan Mukhar Tudun Wada, Matashi daga jam'iyyar adawa ta PDP, ya bayyana rashin jin dadinsa game musanya sunan Maryam Shetty.

"A matsayina na matashi kuma mai goyon bayan ganin an saka matasa a cikin al'amuran shugabanci da siyasa, abin Allah wadai ne kuma abin kunya ne ga shi shugaba Bola."

Zainab Alkali na daga cikin matan da ke da babban buri a tafiyar ta Tinubu, sai dai cire sunan Maryam Shetty ya sa ta fara cire tsammani.

"Wannan labari a gaskiya bai mana dadi ba saboda ya kashe mana kwarin gwiwa da kuma mafarkin da muke da shi na cewa mu ma za mu iya kasancewa wani abu ba tare da an duba karancin shekarunmu ba."

Sai dai wasu 'yan Siyasa irinsu Mahmud Kabir, bayyana gamsuwarsu da suka yi game musanya sunan nata da aka yi.

~ Rukaiya Basha

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG