Majalisar Dattawa ta Soma Muhawara Kan Nadi Hafsan Hafsoshi

Sojojin Najeriya

Shugaban Najeriya ya mika sunayen wadanda ya nada su maye gurbin hafsan hafsoshin fa ya saukar wa majalisar dokokin kasar domin tantancewa da amincewa kafin a saka masu kayan girma.
Da can idan shugaban kasa ya ayyana sunayen wadanda ya zaba su zama hafsan hafsoshi sai ya nadasu ya sa masu lambobin girma daidai da matsayin da ya basu. To amma lamarin ya sake tun da wani dan kasar ya kalubali shugaban a kotun kolin kasar wadda ta yadda da matsayinsa cewa dole ne shugaban kasa ya mika sunayen mutanen ga majalisar dattawa. Ita ce zata tantancesu ta amince ko ta ki amincewa kafin a saka masu lambobin girma.

'Yan majalisar dattawan sun fara tattaunawa kan jerin sunayen da shugaban kasa ya gabatar masu domin su amince kafin ya sa masu lambobin girma. Sanato Ahmad Lawal ya ce abun da ake yi da karya dokar kasa ne domin tsarin mulki ya ba majalisar dattawa dama sai ta amince kafin a yi nadin. Kafin shugaban kasa ya rantsar dasu sai majalisar dattawa ta wankesu tukun na. Wannan karon ya bi doka kuma ya yi daidai.

Sanato Abdullahi Gobir ya ce sai sun gama bincikar mutanen idan sun amince kana shugana kasa ya sa masu lambar girman matsayin da ya basu.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Ta Soma Muhawara Kan Nadin Hafsan Hfsoshi - 2:55