Majalisar Dattawa Ta Sallami Umar Daga Jagorancin Kotun Da’ar Ma’aikata

Yakubu Danladi Umar

An sallame shi saboda zargin aikata almundahana.

A yau Laraba Majalisar Dattawan Najeriya ta yi amfani da sashe na 157 (1) na kundin tsarin mulki, wajen cire Yakubu Danladi Umar daga kan kujerar shugabancin kotun da’ar ma’aikata (CCT) a hukumance.

An sallame shi saboda zargin aikata almundahana.

Cire Umar ya baiwa Abdullahi Bello karbar ragamar jagoranci a matsayin cikakken shugaban kotun a hukumance.

Sanatoci 84 da suka samar da kaso 2 bisa 3 na rinjayen Majalisar Dattawan ne, suka kada kuri’ar amincewa da cirewar, inda suka yanke shawarar mika kudirin ga Shugaban Kasa Bola Tinubu domin daukar mataki na gaba.