Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Ta Kaiwa Sansanin Soja Hari A Borno


Yan Bindiga
Yan Bindiga

Duk da cewa babu tabbatarwa a hukumance game da yawan mutanen da suka mutu, majiyoyi sun ce an hallaka kimanin sojoji 20.

Kungiyar ISIS mai ikrarin jihadi a arewacin Najeriya ta kaddamar da mummunan hari a kan wani sansanin, wanda ya haddasa mace-mace da dimbin asara.

Majiyoyin soja sun shaidawa tashar talabijin ta Channels mayakan ISIS sun kaiwa sansanin sojojin dake garin Kareto na jihar Borno hari da mabambantan makamai a Lahadin da ta gabata.

Duk da cewa babu tabbatarwa a hukumance game da yawan mutanen da suka mutu, majiyoyi sun ce an hallaka kimanin sojoji 20.

Majiyoyin sun kara da cewa an samu zazzafar musayar wuta tsakanin mayakan da dakarun sojin, ciki har da harin kunar bakin waken da aka kai da mota. Sun bayyana cewa harin ya yi sanadiyar lalata wata motar sojoji tare da arcewar wasu daga cikin dakarun sojin.

Sun nuna cewa mayakan sun kwace iko da sansanin tare da banka masa wuta, ciki har da motoci 14.

Majiyoyin sun tabbatar da cewa mayakan sun kwace motoci masu ja da tayoyi 4 da dimbin makamai, ciki har da manyan bindigogi masu sarrafa kansu da kansu kafin su janye daga sansanin.

A wani labarin mai nasaba da wannan kuma, gwamnan jihar Borno ya jajantawa hukumomin sojan game da rasuwar sojoji a garin Kareto.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai da tsaron cikin gida na jihar Borno, Usman Tar, ta ruwaito gwamna Babagana Zulum na cewar harin ya tunawa jihar da irin rashin imanin 'yan ta'addar Boko Haram.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG