Majalisar Dattawa Ta Karbi Bakuncin Ministan Kudin Najeriya

د نیویارک په ټایمزسکویر کې د نوي کال جشن. خلک د ٢٠١٨ کال پای او د ٢٠١٩ کال د پیل جشن لمانځي 

A cigaba da binciken yadda bangaren Gwamnati ke aiwatar da Kasafin Kudin shekara 2016, Majalisar Dattawa ta karbi bakuncin Ministan Kudi Madam Kemi Adeosun, inda ta yi wa Majalisar Dattawa albishir da cewa har yanzu tattalin arzikin Najeriya shine mafi Karfi a Nahiyar Afrika.

Kemi Adeosun, ta bayyanawa majalisar cewa tuni har an fara sakin kudade domin yiwa ‘yan kasa ayyuka kamar yadda shugaba Muhammadu Buhari yayi alkawari.

Sanata Aliyu Mallam Wakili, yana daga cikin ‘yan Majalisar da suka karbi bakuncin Ministan kudin, yace zasu ci gaba da irin wannan gayyata domin sanin matakan da za a dauka don tabbatar da aiwatar da kasafin kudin.

Ministan Kudi Kemi Adeosun, ta tabbatarwa Majalisar Dattawa cewa tattalin arzikin Najeriya na da karfi, saboda haka zai farfado kafin karshen wannan shekara ta 2016.

Saurari rahotan Madina Dauda daga Abuja.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Ta Karbi Bakuncin Ministan Kudin Najeriya - 2'51"