Wannan garambawul dai yazo da bazata a dai dai lokacin da ake ganin kamar kawunan ‘yan kungiyoyin na kara rabewa, idan za a yi la’akari da kace nace da ya biyo bayan wani zama na musamman da Majalisar Dattawa ta yi a kwanakin baya, inda har akayi barazanar tsige shugaba Muhammadu Buhari.
Kwatsam sai ga sanarwar sauya mukaman shugabannin kwamitoci inda shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, ya baiwa masu adawa da shi manyan mukamai. Sanata Kabiru Garba Marafan Gusau ya samu mukamin shugaban kwamitin kula da harkar Man fetur na cikin ‘kasa. Sanata Sulaiman Humkuwi ya samu mukamin ya samu shugaban kwamitin kula da katin zama dan kasa. Sai kuma Remi Tinubu ta samu mukamin ta samu mukamin kwamitin kula da muhalli. Shugabannin kwamitoci 17 aka sauya a Majalisar Dattawan.
A bangaren Majalisar Wakilai kuma kakakin majalisa Yakubu Dogara ya bada sanarwar kwabe shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, Abdulmuminu Jibrin daga mukaminsa, ya kuma maye gurbinsa da Mustapha Bala Dawaki. An dai samu korafi na cewa dan majalisa Abdulmuminu Jibrin ya cusa ayyuka da suka wuce Naira Biliyan Hudu cikin kasafin kudin bana ga mazabarsa ta Babeji da Kiru dake jihar Kano.
Saurari rahotan Madina Dauda daga Abuja.