Takardar kudin Najeriya, Naira, ta sake subutowa kasa a kasuwannin musanyar kudade na kasar, inda a yau alhamis aka canja Dalar Amurka daya a kan Naira 374.
Wannan na zuwa ne a yayin da farashin danyen man fetur ke ci gaba da faduwa kasa a duniya, abinda ke kara takura yawan kudaden kasashen waje da Najeriya ke samu. Kasar dai ta dogara ne kusan kacokam a kan danyen man fetur domin samun kudaden shigarta daga waje.
Masana tattalin arziki sun ce hauhawar farashin kayayyaki a cikin gida da wannan lamarin ke haddasawa kuma, zai gurgunta shirin farfado da tattalin arziki na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, zai kuma kara takura ma jama'ar kasar wadanda tun farko ma ke fama da wahalar tsadar kayayyakin bukatu na yau da kullum.
Hukumar kula da harkokin kididdiga ta Najeriya, ta ce a watan da ya shige, farashin kayayyaki a kasar ya tashi da kimanin kashi 16 cikin 100.
Shugaban kungiyar masu hada-hadar canjin kudade ta Najeriya, Alhaji Aminu Gwadabe, yace akwai bukatar yin garambawul ga sabontsarin da aka bullo da shi na ayyana manyan dillalan kudaden waje, ganin cewa akwai wasu bankuna da kuma su kansu kamfanonin canjin kudade wadanda ba su cikin wannan tsarin.
Mutane da dama da suka tattauna da VOA Hausa sun roki shugaba Muhammadu Buhari da ya mayarda hankali kan wannan batu domin ragewa jama'a radadin tsadar kayayyaki da ake fama da shi a kasar.
Ga cikakken rahoton da Babangida Jibrin ya aiko daga Lagos...