Majalisar Dattawa Ta Fara Sharar Fage Kan Shari’ar Tsige Trump

A yau Alhamis Majalisar Dattawan Amurka ta fara sharar fage kan shari’ar tsige shugaba Donald Trump, tare da zaman farko, da zai hada da ‘yan majalisar wakilai.

'Yan majalisar wakilan, su za su zama masu gabatar da kara kan kudurin tsige shugaba Trump a majalisar dattawan, wacce za ta yanke hukunci a karshe.

Shugaban Amurka Donald Trump

Za a rantsar da Alkalin alkalan katun kolin Amurka, Justice John Roberts, a matsayin wanda zai sa ido kan shari’ar, kana daga bisani ya rantsar da sanatoci 100 na majalisar dattawan.

Dan majalisar wakilai a bangaren ‘yan Democrat, Jerrold Nadler, na daya daga cikin mutum bakwai da za su gabatar da da karar tsige Trump a gaban majalisar Dattawan.

Jerrold Nadler

Ya ce, “mun samu sabbin bayanai da shaidu, wadanda suka nuna cewa shugaban ya yi laifi, sannan mun gano wani yunkuri, da wasu a majalisar Dattawan ke yi, na yin shari’a mara sahihanci.”

Shugaban masu rinjaye, Mitch McConnel ya ce matakin karshe na yau Alhamis, zai sanar da fadar White House da “kirawo shugaban kasa don ya amsa tuhume-tuhumen tsige shi da kuma turo lauyansa.

Mitch McConnell

Za dai a fara ainihin shari’ar ne a ranar Talata mai zuwa.