Har Yanzu Ba Mu Sami Sunayen Wadanda Ake Son Nadawa Ministoci Ba - Majalisar Dattawa

Majalisar dokokin Najeriya ((Facebook/Femi Adesina))

Yau laraba ne aka yi tsamanin shugaban kasa Ahmed Bola Tinubu zai aike da jerin sunayen ministocin sa, amma kuma sai aka sami wasika da ke dauke da sunayen mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar raya arewa maso gabas wato NEDC wadanda Shugaba Tinubu ya nemi majalisa ta tabbatar da su.

Sanata Garba Musa Maidoki daga jihar Kebbi ya yi bayanin cewa majalisar tana dakon sunayen ministocin, ganin cewa doka ta ba shugaban kwana 60, wato wattani biyu domin ya gabatar da sunayen.

A lokacin da Sanata Maidoki ya ke amsa tambayar Muryar Amurka kan ko dokar tana nufin a samu sunayen kuma a tantance su a cikin wattani biyu ne, Maidoki ya ce doka ta tanadi cewa ya bayyana sunayen ne a wattani biyu amma ba'a gindaya cewa dole ne a kammala aiki tantance sunayen a cikin wattani biyu ba.

Manazarta na cewa ana kyautata zaton majalisa za ta sami jerin sunayen ministocin gobe alhamis.

Kokarin samun bayani daga wurin mai ba Shugaban kasa shawara a aiyuka na musamman Dele Alake ya ci tura.

Saurari hirar a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Ta Ce Har Yanzu Ba Ta Samu Sunayen Ministoci Da Ya Kamata A Nada A Kasar Ba