Majalisar Dattawa Na Duba Yiwuwar Daurin Shakaru 15 Ga Duk Mai Biya da Karban Kudin Fansa

Majalisar Dattawan Najeriya ta na duba yiwuwar yi wa dokar rigakafin ta'addanci ta shekara 2013 kwaskwarima inda za a hana biya da karbar kudin fansa.

Dokar ta ce a yi wa mutumin da ya biya kudin fansa da wanda ya karba daurin shekaru 15. To sai dai wannan doka da aka riga aka yi wa karatu na biyu, ta raba kawunan 'yan majalisar dattawan domin akwai wadanda ba su amince da ita ba.

Dan Majalisar Dattawa daga Jihar Imo ta Gabas, Ezenwa Francis Onyewuchi shi ne ya gabatar da kudurin dokar. Dan Majalisar ya ce dokar tana neman gyara dokar ta'addanci na shekara 2013 don haramta biyan kudin fansa ga masu satar mutane.

A cewar Onyewuchi, kudurin na neman maye gurbin sashi na 14 na babban dokar wanda ya ce duk wanda ya tura kudade ya biya ko kuma ya hada baki da wani mai satar mutane ko kuma dan ta'adda don kar6ar kudin fansa don sakin wanda aka tsare, ko aka sace shi, ya aikata babban laifi kuma yana iya fuskantar hukuncin dauri a gidan gyaran hali na tsawon shekaru 15.

To saidai mai fashin baki a al'amuran zamantakewan dan Adam, Abubakar Aliyu Umar ya yi tir da wannan doka inda ya ce zalunci ne kawai ake so a nuna wa talaka. Abubakar ya ce in yan'uwan yan majalisar aka sata, da wuri za su je su kai kudin fansa, saboda suna da kudin amma da yake talaka ba ya samun kudin akai akai suna so su fitar da wata doka mara ma'ana.

Shi ma Sanata Mai Wakiltan Katsina ta Tsakiya, Injiniya Kabir Abdullahi Barkiya ya ce wanan kudurin doka ce kawai da ya ke ganin za a tika da kasa a lokacin da za a bude dandalin sauraren bahasin jama'a, Sanata Kabir Barkiya ya ce shi bai yarda da kudurin dokar ba, amma tunda har an riga an yi masa karatu na biyu, shi zai bayyana ra'ayinsa na kin yarda a lokacin da kowa zai zo dandalin sauraren bahasin.

A nashi nazarin Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba yana ganin akwai dokoki dayawa da aka gyara a Majalisar wadanda har ya zuwa yanzu ba a yi wani amfani da su ba saboda shugaban kasa bai sa hannu akan su ba.

Wadansu suna zargin hauhawar wanan aika aika na ta'addanci kan talauci, siyasa, karancin dokokin da ake da su, rashin aikin yi, hadin gwiwar wasu batagari cikin Jami'an tsaro da kuma son kai.

Saurari cikakken rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dattawa Na Duba Yiwuwar Daurin Shakaru 15 Ga Duk Mai Biyan Kudin Fansa