An samu karin sama da naira Biliyan 500, a kasafin kudin Najeriya na bana, wanda ya kai jimilar naira Triliyan 13 da naira Biliyan 588.
Majalisar wadda ta ayyana kasafin a matsayin kasafin da zai kawo wa al'umma saukin rayuwa, a inda suka amince da kashe naira triliyan 3.3 na kasafin kudin wajen biyan basussuka, sai kuma naira triliyan 4.1 da za'a kashe wajen gudanar da manyan ayyuka.
Majalisar ta amince da ware naira Biliyan 496, ga wasu hukumomin da suka hada da Majalisar Tarraiyya, sai hukumar zabe ta kasa a matsayin abinda za a fara cirewa daga kasafin.
Shugaban kwamitin kula da kasafin kudi, Sanata Barau Jibrin ya yi karin haske, cewa an yi kari a kasafin ne domin a taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar a karkashin shirin NDP, wato National Development Plan a turance na shekara 2021 zuwa 2025.
Sanata Jibrin, ya kara da cewa, ana kyautata zaton Najeriya za ta samu kudin shiga ta haraji har Naira triliyan 8.433 a Shekara 2021.
Amma shi kuwa Sanata mai wakiltan Katsina ta Tsakiya Sanata Kabir Abdullahi Barkiya, cewa yake wannan kasafin zai taimaka wajen farfado da ayyukan yi da zai sa matasa su yi dogaro da kansu.
Ya kara da cewa, an yi kasafin ne a dai-dai lokacin da duniya ke fama da matsalar annobar Korona wadda sanadiyar hakan ta haifar da karyewar farashin danyen Man-Fetur a kasuwar duniya, saboda haka za a sa ido wajen aiwatar da kasafin, ta yadda zai kara wa kasa tsaro, saboda 'yan kasa su samu sukunin more romon demokradiya cikin walwala.
A kasafin da shugaba Buhari ya mika gaban Majalisar an yi shi ne a ma'aunin canji Dalar Amurka daya akan Naira 376, sannan Gangar danyen man fetur akan Dalar Amurka $40. Najeriya za ta hakko Mai kimanin Lita miliyan 1.86 a kowace rana.
Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, ya ja kunnen ma'aikatu da hukumomin gwamnati, da su tabbatar da amfani da amincewar da Majalisar ta yi na kara wa'adin aiwatar da bangaren ayyukan raya kasa na kasafin kudin.
Ga rahoton da Madina Dauda ta hada a cikin sauti.
Your browser doesn’t support HTML5