A yayin da ake ta kai kawo tsakanin Majalisar tarayya da sufeto janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris bayan yin fatali na gayyatarsu sau uku na zuwa yi musu bayani game da kashe-kashen da ke aukuwa a wasu jihohin kasar, majalisar ta ayyanashi a matsayin wanda bai cancanci kowane irin mukami na gwamnati ba. Ko suna da hurumin aikata hakan?
Barista Mainasara Kogo Ibrahim, ya yi mana karin haske dangane da abin da kundin tsarin mulki ya tanadar.
Ya bayyana cewa, a al'amuran Dimokradiyya, kowanne sashe yana da huruminshi kuma yana da karfi da kuma 'yanci.
"Sashe na hudu da sashe na 11 sun ba Majalisar kasa dama da hurumi na yin duk wasu dokoki da suka shafi gyara, da ci gaba da kuma tafiyar da yadda tsarin kasa zai kasance. Saboda haka suna da hurumin gayyatar ko wanene, tun daga masinja har zuwa shugaban kasa, ko da mutum ya kasance ba a karkashin gwamnati ba."
Ya kara da cewa, "suna da hurumin su kirashi domin jin bayani kan duk wani abu da ya shafi zamanshi na dan kasa ko kuma yadda ya ke tafiyar da nauyin da aka dora mai a matsayinsa na jami'in gwamnati."
Bugu da kari, suna da hurumin da za su iya sa a kamo mutum a gurfanar da shi a gabansu.
Sai dai kash, wanda za su iya ba umurnin kamo mutum shi ne sufeton janar na kasa din. To da wuya a ce an kama mai kamawa, kuma ya kamo kanshi ya kawo.
Domin a tsarin Najeriya, sufeto janar na 'yan sanda na karkashin shugaban kasa ne wanda a yadda sashe 130 na tsarin mulki yayi bayani, shine wanda ya ke shugaban gwamnati kacokan na Najeriya.
Saboda haka maganar kudiri na cewa, sufeto janar na 'yan sandan Najeriya bai cancanci ya rike wani ofishi ko na alfarma ko kuma na cancanta ba, sun zafafa a cewar baristan. Domin ya kamata a ce su bukaci shi shugaban kasa ya gabatar da shi jami'in da ke karkashinsa ko kuma su ba shugaban kasa umarnin na bukatarsu dangane shi sufeton 'yan sandan.
Saurari rohoton hirar Barista Mainasara tare da wakiliyarmu Medina Dauda
Your browser doesn’t support HTML5