Mai Yiwuwa Amurka Ta Fice Daga Yarjejeniyar Takaita Makaman Nukiliya

Alamu na nuna cewa mai yiwuwa Amurka ta fice daga yarjejeniyar takaita makaman nukiliya da ta kulla da babbar abokiyar hamayyarta Rasha.

Bisa ga dukkan alamu, gwamnatin shugaban Donald Trump na shirin ficewa daga wata yarjejeniyar da aka rattabawa hannu a shekarar 1987, ta takaita makaman nukiliya tsakaninta da Rasha.

Wannan alama ta ficewa daga yarjejeniyar ta fara bayyana ne bayan wata ganawa da mai bai wa shugaban Donald Trump shawara a harkar tsaro John Bolton ya yi da shugaba Vladimir Putin.

Shugaba Donald Trump ya zargi Rasha da karya ka’idojin da aka saka a yarjeneniyar ta makamai masu cin matsakaicin zango, wadanda ya ce har yanzu Rasha na amfani da su.

Mr. Bolton ya kira wannan matakin a mtsayin karya ka’idar a matsayin dadaddiya kuma mai zurfi.

Tsohon shugaban Tarayyar Soviet, Mikhail Gorbachev, da tsohon shugaban Amurka Ronald Reagan, ne suka rattaba hannu a yarjejeniyar makaman nukiliyar a shekarar 1987.

Yarjejeniyar dai ta hanna Amurka da Rasha kera makamai, da gwaji har ma da tara makaman masu tafiyar kimanin kilominta 500 zuwa 5,000.