Mai Ya Malale A Tsibirin Mauritius Dake A Tekun India

Hoton taurarin dan Adama na malalar mai

Tsibirin Mauritius dake gabar tekun India ya ayyana dokar tabaci a kan muhalli, bayan kwanaki da tan mai yawa na man fetur ya tsiyaye a cikin wani jirgin ruwa mallakar kasar Japan a kan teku.

Firai Ministan kasar, Pravind Jugnauth shien ya sanar da wannan labari da yammacin jiya Juma’a, yayin da hotunan taurarin dan Adam suka nuna bakin mai kwance kan ruwan tekun yankin abin da gwamnati ta kira da mai tsanani.

Mauritius ta ce jirgin ruwan na dauke da kusan tan dubu hudu na mai yayin da ya makale a kan tekun a ranar 25 ga watan Yuli.

Jugnauth ya ce gwamnatin sa tana kira ga kasar Faransa ta kawo mata dauki, yana mai cewa tsiyayar man wani babban hadari ne ga kasar mai mutane miliyan daya da dubu dari uku da ta dogara kacokam a kan yawon bude ido wanda kuma cutar coronavirus ta yi mata illa.

Ya ce kasar mu bata da kwarewa da kwararrun da zasu janye jirgin, a dan haka ya ce ya shigar da bukatar neman taimako daga Faransa da shugaba Emmanuel Macron, inji Firai ministan.