Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

WHO Ta Tura Tawaga Afirka Ta Kudu


Wata tawagar kwararru daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta isa Afirka ta Kudu domin taimakawa kasar dakile yaduwar cutar ta coronavirus da ke ci gaba da yaduwa. 

Ziyarar tawagar na zuwa ne a daidai lokacin da cutar ta COVID-19 ke ci gaba da yaduwa a sassan duniya.

Cikin wata sanarwa da ta fitar, hukumar ta ce kwararru 43 da suka kware a fannoni daban-daban kamar na dakile yaduwar annoba, bin diddigi, da samar da rigakafi, za su tallafawa kwamitin da kasar ta Afirka ta Kudu ta kafa domin yaki da cutar.

Abu na farko da za su fara yi shi ne, yin nazarin ayyukan da ma’aikatar lafiyar kasar ke yi kafin su ba da tasu gudunmuwar a yankunan da annobar ta fi shafa, wadanda suka hada da Eastern Cape, Free State, Gaunteng, Kwazulu Natal da kuma Mpumalanga.

Hauhawar adadin masu kamuwa da cutar da kasar ke gani, ya sa yawan wadanda suka kamu da cutar ya kai dubu 530, lamarin da ya sa Afirka ta Kudun a matsayin kasa ta biyar da ta fi fama da cutar a duniya.

Izuwa yanzu, mutum 9,200 kasar ta tabbatar sun mutu sanadiyyar cutar ta COVID-19.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG