WASHINGTON. D. C. - Yayin da Netanyahu da ministan tsaronsa, Yoav Gallant, ba sa fuskantar kame cikin gaggawa, sanarwar da babban mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ya yi, wata alama ce ta alama da ta zurfafa warewar Isra'ila kan yakin Gaza.
Mai gabatar da kara na kotun, Karim Khan, ya zargi Netanyahu, Gallant, da shugabannin Hamas uku; Yehia Sinwar, Mohammed Deif da Ismail Haniyeh da aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a zirin Gaza da Isra'ila.
Netanyahu da sauran shugabannin Isra'ila sun yi Allah wadai da matakin da cewa abin kunya ne da kuma nuna wariya.
Shugaban Amurka Joe Biden ya kuma caccaki mai gabatar da kara tare da goyon bayan ‘yancin Isra’ila na kare kanta daga Hamas.
Kwamitin da ya kunshi alkalai uku ne za su yanke shawarar ko za su bayar da sammacin kama su da kuma ba da damar ci gaba da shari’ar, wanda alkalan sukan dauki watanni biyu kafin su yanke irin wannan hukunci.
-AP