Sarkin yace a wannan aikin hajjin bitoci da fadakarwa da aka yiwa maniyatta kafin su taso zuwa kasa mai tsarki sun yi tasiri saboda an yi anfani dasu.
An fadakar da alhazai kan kiyaye dokokin kasar Saudiya tare da jin tsoron Allah. Tun farko an ja masu kunnuwansu da su maida hankulansu kan abun da ya kaisu kasa mai tsarki.
Akan shawarar da sarkin zai iya ba alhazan sai yace ya kan fadawa alhazan basu da wata kasa da ta wuce Najeriya. A halin yanzu babu abun da kasar ke bukata irin addu'a musamman canjin gwamnati da aka samu.
Ya kira alhazan da su hakura su jira sarautar Allah amma su cigaba da yiwa kasar da shugabanninta addu'o'i. Kada mutane su zama masu gaggawa, amma su zama masu hakuri. Su roki Allah ya ba kasar zaman lafiya.
Dangane da abun da ya sa sarkin yake zama da alhazan har sai sun kammala duk abubuwan da suke yi ganin nauyin shugabanci dake kansa sai yace amana daya take. Gwamnan jihar Bauchi ya ce ya jagoranci alhazan jihar zuwa aikin hajji saboda haka amana ce aka bashi wadda wajibi ne ya kareta. Yace ba ya son ya bar alhajin Bauchi a baya ba tare da ya ga komi ba. Haki ne kansa ya tabbatar abun da ya fada abun da ya gani ne. Ko gwamna bai tambayeshi ba Allah zai tambayeshi. Yace yadda suka zo tare su koma tare wannan shi ne kwanciyar hankalinsa.
Ga rahoton Nasiru damu El-Hikaya.
Your browser doesn’t support HTML5