Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bukaci Mahajjata Su Yiwa Najeriya Addu’a


Hajj
Hajj

A Najeriya, akalla mahajjata 1,900 daga jahar Adamawa ake sa ran za su je kasa mai tsarki domin sauke farali, wadanda aka yi kira da su tuna da kasarsu a addu'oinsu.

Mai martaba Lamidon Adamawa, Dr. Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, ya yi kira ga maniyyata hajjin jahar da su yiwa Najeriya addu’a yayin da suke shirin tafiya kasa mai tsarki.

Lamidon Adamawan ya yi wannan kira ne yayin da ya ke bankwana da maniyyata hajji su 1,900 daga jahar wadanda za a fara jigilarsu.

“Ku yiwa kawunanku addu’oi, ku yiwa kasarku ku yiwa shugabanninku, Allah ya kaiku lafiya ya maido da ku lafiya, Allah kuma ya sa hajjinku karbabbe ne.” in ji Mai martaba Barkindo.

Yayin da ya ke na shi jawabin bankwanan, gwamnan jahar Sanata Muhammadu Bindo Jibrilla, ya ce gwamnati ta yiwa mahajjata tanadi na musamman tun daga nan gida Najeriya zuwa kasa mai tsarki.

“Duk wanda zai shiga jirgi, za a bashi dan kaset, wanda za ku saurara domin ya nuna muku yadda za ku yi aikin hajji cikin natsuwa ba tare da kun yi kuskure ba.”

Dangane da batun wadanda suke korafin wasu ma’aikatan hukumar walwalar alhazai sun damfaresu, Sakataren hukumar Engineer Umar, ya ce za su dauki mataki kan hakan duk da cewa wadanda ake zargi da yin damfarar ba cikakkun ma’aikatansu ba ne.

Ga karin bayanin wannan labari a rahoton wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz daga Yola, jahar Adamawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG