Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alhazan Najeriya Sun Shirya Hawan Arafa Gobe Laraba


Alhazai
Alhazai

Shugaban hukumar alhazai ta Najeriya Barrister Abduulahi Mukhtar Muhammad ya zanta da ,uryar Amurka akan shirin alhazan Najeriya dake aikin ibada na wannan shekarar a kasa mai tsarki

Shugaban hukumar ya bayyana halin da maniyattan Najeriya su 66,000 ke ciki yayin da ake gaf da hawan arafa gobe Laraba.

Yace alhazan Najeriya na cikin shiri da damarar fita domin zaman Minna da kuma zuwa hawan arafa. Hukumar alhazai ta kasa da hukumomin jihohi da malamai da suke aikin hajji sun tattauna kan hanyoyin da za'a bi a ci nasara a fitar Minna da hawan arafa da kuma zaman da za'a yi na jifan jamra.

Yace taron da aka yi a karkashin jagorancin mai martaba sarkin Kano ya cimma matsaya akan cewa hakika bai sabawa shari'a ba alhazan Najeriya su fara fita daren bakwai ga wata har zuwa takwas.

An inganta tantunan da alhazan zasu yi anfani dasu da kara wuraren kewayawa daga wurin tsuguno zuwa na boli da yin alwala da wanke hannu. Haka kuma sabbin shimfida aka sa a wuraren. Amma naura mai bada sanyi ta gaza saboda haka alhazan zasu ji zafi. Dole alhazai su shirya su fuskanci zafin.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG