Mai Mala Zai Dawo Najeriya A Matsayin Gwamnan Jihar Yobe Ne Kawai, Ba Shugaban Rikon Jam’iyyar APC Ba - El-Rufai

Gwamna El Rufai (Facebook/El Rufai)

El-Rufai ya kara da cewa shugaba Buhari ya umarce su da su nemi hanyar da ta dace kuma bisa ka'ida wajen sauke Mai Mala Buni a matsayin shugaban rikon jam’iyyar ta APC.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar kaduna ya tabbatar da cewa takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni, ba zai dawo Najeriya daga tafiyar da ya yi a matsayinsa na shugaban rikon kwaryar jamiyyar APC ba illa a matsayinsa na gwamnan jiharsa ta Yobe.

Wannan lamari dai ya fara fitowa fili ne a ranar Litinin da ta gabata inda aka ga gwamna Abubakar Sani Bello, na jihar Neja ya dare kujerar rikon kwaryar jam’iyyar a matsayin mukaddashi, abin da wasu ke ganin lamarin na kama da juyin mulki.

Sai dai da ‘yan jaridu suka ma sa tambaya bayan rantsar da wasu shuwagabannin jam’iyyar a matakin jihohi da ya yi a sakatariyar jam’iyyar a babban birnin tarayya Abuja, gwamna Sani Bello, ya ce yana aiki ne kawai a madadin Mai Mala saboda tafiyar da ya yi ba ya ofis ne.

Haka kuma, rahotanni sun yi nuni da cewa a wata tattaunawar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi da gwamnoni a yayin wani taro da ya gudana a birnin Abuja kafin shugaban ya yi tafiya zuwa Ingila don duba lafiyarsa a ranar Lahadi, ya ba su umarnin tafiyar da jam’iyyar yadda ya kamata duk da cewa Mai Mala Buni ba ya kasar.

Gwamna El-Rufai ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke amsa tambayoyi a cikin shirin siyasa a yau wato "Politics Today," na gidan talabijan na Channels inda ya ce, Bello yana da goyan bayan gwamnoni 19 cikin 23 dake zaman mambobin jam’iyyar APC mai mulki ke dashi tare da shugaban kasa.

El-Rufai ya kara da cewa shugaba Buhari ya umarce su da su nemi hanyar da ta dace kuma bisa ka'ida wajen sauke Mai Mala Buni a matsayin shugaban rikon jam’iyyar ta APC kuma kwamitin gudanarwa jam’iyyar ta zai nada gwamna Bello a taron da za ta yi a mako mai zuwa da kuma cire Buni daga kan kujerarsa.

A cewar El-rufai, akwai tabbacin cewa Mai Mala ba zai dawo Najeriya a komai ba sai gwamnan jihar Yobe wanda shi ne ainihin matsayinsa da kowa ya sani.

Haka zalika, El-Rufai ya kara da cewa kwamitin rikon kwaryar jam’iyyar APC da zai shirya zaben kasa, ya tabbatarwa Sanata John James Akpanudoedehe cewa zai shirya taron majalisar zartarwar jam’iyyar a ranar da kwamitin ya cimma a bisa umarnin shugaba Buhari, lamarin da ya fusata shi ya fice daga taron ba’a gama ba.

Gwamna Bello ne ya ba da shawara kan saka ranar yin taron majalisar zartarwa ta jam’iyyar a yayin taron kwamitin rikon kwaryar inda sakatare Akpanudoedehe ya nuna rashin yardarsa.

Amma an samu yardar ragowar mutanen kwamitin, kuma ya tabbatar da cewa kwamitin ba zai yi komai ba sai ya tuntubi ministan shari’a kuma Antoni-Janar na tarayyar kasar, Abubakar Malami.

Har yanzu dai duk kokarin ji ta bakin fadar shugaban Najeriya da gwamna Mai Mala Buni don jin matsayarsu kan abin da ke faruwa, ya ci tura.