A wasikar ajiye aikin, Flynn ya ce bisa kuskure bai yi cikakken bayani ga Mataimakin Shugaban Kasa Mike Pence da sauran jami'an ba game da tattaunawa ta waya da ya yi da Jakadan Rasha dake Amurka.
Rahotannin Jaridun Washington Post da New York Times na ranar Jumma'a sun ce Flynn ya tattauna da Jakadan Rasha kan takunkumin da gwamnatin Obama ta kakaba ma Rasha, duk kuwa da karyatawar da gwamnatin Trump ta yi ta yi.
'Yan Majalisar Dattawan Amurka na jam'iyyar Democrtat da dama sun yi ta kiraye-kirayen a binciki Flynn, a yayin da kuma wasu ke cewa ya kore shi kawai kuma bangaren leken asirin kasa ya yi nazari kan matsayinsa a bangaren na tsaro.
Wasu mutane tara, wadanda su ka bukaci ya sakaya sunayensu, wadanda aka ce jami'an gwamnati ne na da da yanzu, sun gaya ma jaridar ta Washington Post cewa lallai Flynn da Jakadan Rasha a Amurka Sergey Kislyak sun tattauna kan batun takunkumin da gwamnatin Obama ta kakaba ma Rasha.