Mahukuntar Kasar Amurka Sun ce Rasha ta Fara Kai Hari ta Sama a Kasar Syria

Wannan dai na faruwa ne kwanaki biyu bayan da shugaba Puttin da Barrack Obama suka cimma matsaya a birnin New York

Mahukuntar kasar Amurka sunce Rasha ta fara kai hari ta sama a kasar Syria, awa daya bayan da majilisar dokokin kasar ta Rasha ta amince da rokon da shugaba Vladimin Puttin yayi na girke sojojin dake goyon bayan shugaba Bashar Al-Asssad.

Shugabannin da suka yi Magana game da wannan batu kuma basu yadda a ambaci sunan sunan su ba, suka ce sojojin Rasha sun sanar da Amurka cewa suna shirin kai hari a wani wuri kusa da birnin Homs.

Wannan dai na faruwa ne kwanaki biyu bayan shugaba Puttins da takwaran sa na nan Amurka Barrack Obama sun cimma matsaya a birnin New York cewa zasu yi aiki kafada da kafada akan duk wani batu da ya shafi kasar ta Syria.

Sai dai kuma mai Magana da yawun gwamnatin kasar na Rasha ya fada a gidan talabijin din kasar cewa amincewar da majilisar dokokin kasar tayi wata dama ce ko kuma ma umurni cewa sojojin sama na Rasha suna iya aiki a Syria.

Dama dai Russia na ta kara inganta harkokin sojan ta a kasar na Syria, musammam da makamai, da Karin sojojin da take ta jibgewa a arewa maso kudancin kasar ta Syria a cikin yan makonnin nan.