A Yau Talata ne mahukuntan gwamnatin tarayyar Amurka suka fara tuhumar wata mata ‘yar Rasha akan aikata laifin yiwa Amurka zagon kasa da kuma laifin yin aiki a matsayin jami’ar gwamnatin wata kasa dake da alaka da kitsa yin shisshigi a siyasar Amurka a zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2016.
WASHINGTON D.C —
An kama Maria Butina, wata mai kare hakkokin mallakar bindiga dake da alakar kud-da-kud da kungiyar kare muradan mallakar bindiga ta kasa ranar Lahadi akan zargin cewa, wata ‘yar kasa mara rijistar na aiki a Amurka ba tare da ta sanar da hukumomin shara’ar kasar ba, kamar yadda doka ta tanada.
Ana zargin Butina, ‘yar shekaru 29 da haihuwa, da yin aiki a sirrance da masu fada-a-ji a Amurka da kuma, kutsawa cikin harkokin kungiyoyin siyasar Amurka, kamar NRA, da zummar cimma muradan Rasha a Amurka.
A cewar sanarwar tuhumar, Butina ta yi wasu ayyuka bisa ga umurnin wasu manyan jami’an gwamnatin Rasha. Sai dai sanarwar bata bayyana sunayen jami’an na Rasha da take yiwa aiki ba.