Sama da mutum dubu 500 a yankunan gabar tekun jihohin Alabama da Florida a nan Amurka, na zaune babu wutar lantarki a yau Alhamis, bayan da mahaukaciyar guguwar Sally da ta yi barna ta ratsa ta yankunan.
Mahaukaciyar guguwar ta Sally ta sauka ne a ranar Laraba da safe a guguwa mai mataki na 2 a kusa da gabar tekun Gulf, na jihar Albama, kuma a hanakali ta mamaye sassan jahar kana har zuwa cikin yankin panhadle na jihar Florida.
Guguwar mai gudun kilomita 165 a cikin sa’a guda dauke da ruwan sama kamar da bakin kwarya ta haddasa ambaliyar ruwa a kananan garuruwa da dama, ta kuma ture turakun wutar lantarki tare da lalata gidaje da wuraren kasuwanci.
Magajin garin Orange Beach da ke jihar Alabama, Tony Kennon, ya shaidawa kafafan yada labarai cewa guguwar ta yi sanadiyar mutuwar mutum daya sannan wani mazaunin yankin ya bata.
Ma’aikatan agaji sun ceto akalla mutum dari 377 a karamar hukumar Escambia da ke jihar Florida, wanda ya kasance wuri ne na shakatawa bayan da guguwar ta Sally ta zubar da ruwa mai tsirin centimita 61 a daukacin karamar hukumar.