Maharba A Arewa Maso Gabashin Najeriya Sun Koka

A wani mataki na sake daura damarar yaki da burbushin ‘yan kungiyar Boko Haram, hadakar kungiyar maharban Najeriya, sun zabi sababbin shugabanin maharba na shiyyar arewa maso gabashin Najeriya.

Maharba kan taka muhimmiyar rawa a yaki da masu tada kayar baya na Boko Haram, baya ga amfani da su da ake yi wajen yaki da bata gari musamman barayin shanu. To sai dai kuma maharban sun koka da cewa an maida su saniyar ware kamar yadda Mr Philip Ngurore, dake cikin kwamandojin maharban jihar Yobe, ya bayyana.

Maharban dake bitar irin rawar da suke takawa a harkar tsaro musamman a jihohin arewa maso gabas da matsalar Boko Haram tafi shafa, sun ce sun dau wannan mataki ne domin samun hadin kai.

Maharban sun tabbatar da wannan mataki ne a babban taron da suka saba gudanarwa duk shekara mai taken Salala, inda sukan taru don daukan rantsuwa.

Alhaji Muhammad Usman Tola, dake zama sabon shugaban kungiyar na shiyar arewa maso gabas, ya nuna farin cikinsa tare da saba layar cewa zasu hada kai don kwalliya ta biya kudin sabulu. Kamar sauran maharba, Modibbo Idris Usman, shine sakataren gayyata da tsare tsaren kungiyar ya yaba da wannan nadi da aka yiwa Usman Tola.

Bikin salalan na bana ya kayatar matuka inda maharba daga ciki dama wajen Najeriya suka halarta.

Ibrahim Abdul’aziz nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Maharba A Arewa Maso Gabashin Najeriya Sun Koka