Akalla fararen hula 15 ne aka kashe wasu biyu kuma suka jikkata a yayin wani harin ‘yan ta’adda da aka kai a wata cocin Katolika a lokacin da ake gudanar da taron sujada a ranar Lahadi a arewacin Burkina Faso, in ji wani babban jami’in cocin.
“Mun sanar da ku harin ta’addancin da aka kai kan mabiya darikar cocin Katolika dake kauyen Essakane a yau 25 ga watan Fabrairu, a yayin da suka taru domin yin addu’o’I a ranar lahadi,” in ji limamin cocin reshen Dori, Jean-Pierre Sawadogo a wata sanarwa da aka aika wa kamfanin dillancin labaran AFP.
Ya kara da cewa adadin wadanda suka mutu ya kai mutun 15 wasu 2 kuma suka jikkata.
Da yake kira kan samar da zaman lafiya da tsaro a Burkina Faso, Sawadogo ya yi tir da "wadanda ke ci gaba da kashe-kashe a kasar.
Kauyen Essakane, inda aka kai harin, yana a yankin da ke da "iyakoki uku" a arewa maso gabashin kasar, a kusa da kan iyakokin kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.
Wannan dai shi ne hari na baya-baya a cikin jerin hare-haren da ake zargin kungiyoyin masu da'awar jihadi da ke fafutuka a yankin ne suka kaisu, inda wasu daga cikinsu suka kai hari kan majami'un Kiristoci yayin da wasu ke da hannu wajen sace malaman addinin Krista.
Burkina Faso dai na daga cikin yankin Sahel da ke fama da tashe tashen hankula tun bayan yakin basasar Libya a shekara ta 2011, sannan kuma a shekara ta 2012 mayakan IS suka karbe arewacin Mali.
Rikicin masu jihadin ya bazu zuwa kasashen Burkina Faso da Nijar tun daga shekarar 2015.
A lokacin da Kyaftin Ibrahim Traore ya karbe mulki a shekarar 2022, wannan ne karo na biyu da aka yi juyin mulki a kasar kasa da shekara guda, duka biyun takaddama akan gazawar gwamnati wajen murkushe masu jihadi ne suka haddasa su.
Kimanin mutane 20,000 ne aka kashe a Burkina Faso a wannan tashin hankalin, yayin da sama da miliyan biyu suka rasa muhallansu.