Kamar yadda al’umman yankin suka tabbatar,mayakan na Boko Haram sun kai farmaki ne ta yankin kauyen Yahza dake tsakanin jihohin biyu inda suka yi barna masu dinbin yawa, ciki har da gidaje da kuma amfanin gona.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, yace yanzu haka al’ummomin wadannan yankuna na cikin wani mawuyacin hali na zaman dar-dar da kuma fargaba.
Koda yake kawo yanzu hukumomin tsaro basu yi Karin haske ba kan lamarin, amma kuma dan Majalisar Wakilai dake wakiltar yankin Madagali da Michika, Hon Adamu Kamale,ya tabbatar da wannan sabon harin ya kuma koka game da sabbin hare haren da ake kaiwa yankunan, ya kuma bukaci da a kara yawan dakaru a garuruwan.
Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5