Mahajjatan Nijeriya Hudu Sun Rasu

  • Ibrahim Garba

Mahajjata a Saudiyya

Mahajjatan Nijeriya hudu sun rasu yayin da Hukumar Jin Dadin Alhazan Nijeriya ke ba da himma wajen kula da lafiyar Alhazan Nijeriya.
Alhazan Nijeriya kimanin hudu ne Hukumar Jin Dadin Alhazan Nijeriya ta tabbatar cewa sun mutu a Saudiyya saboda dalilai daban-daban ciki har da wata ‘yar jihar Bauchi da Allah ya ma ta cikawa sanadiyyar faduwa daga benen da ta yi.

Da ya ke wa ‘yan jarida bayani, ciki har da wakilinmu na jihar Naija da a yanzu ke Saudiyya Mustapha Nasiru Batsari, Kwamishinan Hukumar Alhazan Mai Kula da Sashin Sadarwa, Dr. Bello Okenwa ya ce sauran mahajjatan da su ka rasu sun fito ne daga jihohin Jigawa da Zamfara da Oyo, inda aka sami wata ‘yar jihar da ta mutu sanadiyyar rashin lafiya.

Wakilin na mu ya ruwaito shugaban tawagar likitocin Nijeriya Dokta Sabo Muhammad ya na bayyana cewa Alhazan Nijeriya 4500 ne aka dubi lafiyarsu sanadiyyar rashin lafiya kuma an yi jinyar wasu har an kwantar da wasu kimanin hamsin da biyar zuwa sittin a asibitin Nijeriya.

Tuni kuma aka shiga yin hudubar tsabta ga mahajjatan Nijeriya. Sheikh Sani Idris daga jihar Naija na daga cikin Malaman da ke irin wannan hudubar. Sheikh Idris ya kawo Hadisan da ke nuna wajibci da kuma alfanun tsabta duniya wa Lahira inda ya jaddada cewa tsabta cikamakon addini ne.

Your browser doesn’t support HTML5

Mahajjatan Nijeriya Hudu Sun Rasu - 2:32

.