Duk kayan da aka saya musamman wadanda ba a yarda a shiga da su jirgi ba irin karafuna, wukake har ma da gorunan ruwan zamzam, a kan karbe su a filin jirgin da hakan ke jawo asarar da za a iya kauce ma ta.
Shugaban Hukumar Alhazan Abdullahi Mukhtar ya bayyana nau’in kayan da ba su dace alhazan su dauka ba, ciki har da ‘yan tsakuwoyin muzdalifa. Ya ce akwai abubuwa da dokokin su ka yarda a shiga dasu a cikin jirgin sama, a don haka duk wani abu sabanin abubuwan da doka ta gindaya za a kwace.
Shi ma jami’in tsaron alhazan Bashir Jazuli ya koka ga yadda musamman alhazai mata kan shake jikinsu da kaya da hakan kan jefa hatta rayuwarsu a hatsari. Ya bayyana takaici a kan yanda alhazai tsofaffi ke kuka a filin jirgi idan aka kwace musu kaya saboda sun saba ka’ida ta daukar kayan da bai fi kilo takwas ba.
Bashir Jazuli ya yi kira ga wakilan alhazai na jihohi da na kananan hukumomi da su wayar da alhazan yankunansu domin guje wa irin wannan asara.
Yanzu dai Hukumar Alhazan ta dawo da alhazai fiye da dubu ashirin gida a sawun jirage 42, da hakan ke nuna kimanin rabin alhazan sun dawo.
Ga dai rahoton wakilinmu Saleh Shehu Ashaka daga Abuja:
Your browser doesn’t support HTML5