WASHINGTON, DC - Mahajjata miliyan daya daga sassa daban-daban na duniya ne suka taru a yau Alhamis a birnin Makkah na kasar Saudiyya don gudanar da aikin hajjin na farko, wanda ya zama aikin hajji mafi girma na addinin Musulunci tun bayan barkewar cutar coronavirus, wadda ta janyo dakatar da aikin na shekara-shekara, wanda ke cikin shika shikan addinin Musulunci.
Hajji wani aiki ne mai mahimmanci na akalla sau daya a rayuwa ga dukkan Musulmi mai hali da lafiya, wanda ke daukar muminai bisa tafarkin da Annabi Muhammad (SAW) ya bi kimanin shekaru 1,400 da suka gabata. Mahajjata za su kwashe kwanaki biyar suna gudanar da ayyukan ibada da niyyar samun kusanta ga Allah.
Hakan ya hada da yin addu'a ana kewaye Ka'aba, wurin ibada mafi tsarki a Musulunci. A tsakiyar harabar babban masallacin Juma'a a ranar Alhamis, dubban maniyyata da ba sa rufe fuskokinsu ba suna zagaye dakin Ka'aba.