Mahaifiyar Yarinyar Da Mutum 7 Suka Yi wa Fyade Ta Nemi Gwamnati Ta Bi Mata Kadi

Zanga zangar Kyamar Fyade A Kano

Wata mata a Sokoto ta koka tare da neman a bi wa ‘yarta hakinta akan fyade da ta ce wasu mutane bakwai suka yi wa ‘yarta, kuma yanzu suna fuskantar barazana da kyama a unguwar da suke zaune.

Yarinyar mai kimanin shekara 11 da ke zaune a unguwar Tudun Wada a jihar Sokoto wadda ake zargin mutane bakwai sun yi wa fyade ta ce ba ta zuwa makaranta kullum tana zaune a gida.

Mahaifiyar yarinya Hajiya Jamila ta ce sun kai karar mutanan bakwai a ofishin ‘yan sanda na Dadin Kowa domin a bi musu hakkin su.

Rahotanni sun ce dukkan mutum bakwan sun amsa cewa sun yi lalata da yarinyar, inda aka tura su kotu ta Konnawa inda ita mai shari’ar ta ce ba ta da hurumin yanke musu hukunci.

Hajiya Jamila ta ce ta nemi babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan Shari’a na jihar Sokoto da ya sa hannu ga matsalar kuma ya nuna mamaki akan bayar da mutanen beli kuma ya ce za'a yi duk abin da ya kamata.

Wakilin Muryar Amurka ya nemi jin ta bakin kwamishinan shari'ar na jihar Sokoto amma ta bakin mai taimaka masa ga ayyukkan ofis, ya ce ba zai samu ganinsa ba a lokacin domin yana ganawa da al'umomi daban-daban.

Wani lauya mai taimakawa marasa karfi da ke fuskantar shari'a, Barista Mansur Aliyu, ya ce sau da yawa ake samun tsaiko ga irin wadannan shari'u domin ‘yan sanda da ke gudanar da bincike basu da karfin shigar da karar irin wadannan laifuka a manyan kutuna, su kuma kananan kotuna ba su da hurumin sauraren su.

Mahifiyar yarinyar ta ce duk da yake an kai yarinyar asibiti an binciki lafiyar ta lokacin da abin ya faru, kuma an yi mata magani na matsalar da ta samu, suna neman daukin gaggawa domin halin kunci da ta ce suke ciki, domin mahaifin yarinya ya dade da rasuwa.

Yanzu dai ganin yadda a watannin baya-bayan nan matsalar fade ma 'yan mata kanana ta yawaita a Najeriya, an kaddamar da shirin tattara bayanai kan duk wata aika-aika mai nasaba da cin zarafin mata.

Saurari rahoton Muhammadu Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Mahaifyar Yarinyar Da Mutum 7 Suka Yi wa Fyade Ta Nemi Gwamnati Ta Bi Mata Kadi