Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zauren Tattaunawar VOA Da Aka Yi Kan Fyade


Wasu bakin da suka halarci zauren tattaunawar VOA kan fyade
Wasu bakin da suka halarci zauren tattaunawar VOA kan fyade

A dai-dai lokacin da kungiyoyi ke fitowa domin tofa albarkacin bakinsu dangane da matsalar fyade a Najeriya, Sashen Hausa na Muryar Amurka ya shirya wani zauren tattaunawa kan batun.

Batun cin zarafi mata da kananan yara ta hanyar yi musu fyade ya zama ruwan dare a arewacin Najeriya inda aka yi ta samun rahotanin da ke nuna yadda ake tauyewa yara hakkinsu.

Mutane daga bangarori da dama ne suka halarci zauren a ranar 23 ga watan Yuli domin tattauna yadda lamarin ke kara muni a kasar da kuma yadda ya kamata a shawo kansa.

Mahalarta zauren sun danganta matsalar da abubuwa kamar tallar da ake sa yara mata da kuma sakacin wasu iyaye.

Daya daga cikin iyaye mata da suka halarci taron Hajiya Fathi’a Sha’ibu, uwargidan tsohon gwamnar jihar Filato da Neja a zamanin mulkin marigayi Sani Abacha, ta bayyana talauci a matsayin daya daga cikin abubuwan da ke sanya iyaye na dora wa yaransu talla.

Wasu bakin da suka halarci zauren tattaunawar VOA kan fyade
Wasu bakin da suka halarci zauren tattaunawar VOA kan fyade

Hajiya Maryam mamman Nasir shugaban wata kungiyar da ke fadi-tashi wajen ganin an yi yaki da wannan masifa, ta ce "na farko ya kamata mu zagaya mu ilmatar da iyaye mata kan illolin barin yaransu su fita talla, don sai yaro ya fita ne ma za a ganshi har a yi masa illa."

"Za mu kuma yi kira ga Malamai su fara wa'azi da kakkausar murya ga iyaye da kuma 'yan uwan da ke yi wa yaransu da kannensu fyade."

Shi kuwa dan majalisar tarayya da ke wakiltar mazabar Maiyama, Koko da Besse na jihar Kebbi Honorable Shehu Mohammad, ya bayyana takaicin al’amarin da kuma goyon baya wajen ganin an saka doka mai tsauri da za ta hukunta duk wanda aka kama da laifin fyade a kasar.

Wakilan sashen hausa, Medina Dauda da Nasiru El-Hikaya
Wakilan sashen hausa, Medina Dauda da Nasiru El-Hikaya

Daga karshen Hajiya madina Dauda da Nasiru El-hikaya da suka jagoranci zauren taron sun mika godiya ga wadanda suka samu halartar taron a madadin hukumar VOA da suka amshi goron gayyatarsu.

Saurari cikakken rahoto kan zauren a cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00


Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG