KANO, NIGERIA - Mahaifiyar marigaya Ummita, Malama Fatima Zubairu ta nuna godiya ga Allah kan kasancewar hukuncin da aka yanke.
“Na gode wa Allah da ya nuna min wannan rana ina matukar farin ciki,” ta bukaci Allah ya jikan Ummita ya kuma sakawa wadanda suka tsaya a kan wannan sharia har aka cimma nasara.
Mai sharia Sunusi Ado Ma’aji ne ya yanke wannan hukunci bayan kama saurayin na Ummita Mr. Frank Geng da laifin aikata kisan kai.
Idan za’a iya tunawa dai an kama tare da tsare Geng-Quangrong ne bayan kama shi a watan Satunban shekarar 2022 da laifin kashe Ummita mai shekaru 22, a gidansu da ke Janbulo a karamar hukumur Kumbotso.
Bayan yanke hukuncin, Kwamishinan Shari'a na jihar Kano, Haruna Dederi, ya bayyana wa manema labarai cewar an kammala bincike sannan an kama shi da laifin kisa.
"Shine alkalin wannan kotu yayi wannan hukunci na kama Frank da laifin kisa kuma hukuncin kisa ne duk wanda yayi kisa shima hukunci a kashe shi, kuma yayi hukuncinsa a haka cewa za’a rataye shi ne har sai ya daina motsi ya rasa rai abinda alkali ya fada kenan.
"Ita sharia tana da farko tana da karshe, abubuwan da aka iya bi aka gano kafin sharia da sune aka kafa hukunci sannan abubuwan da suka gabata da shine aka gabatar da wannan hukunci kuma mutum ba zai aikata laifi ba a kuma barshi yana yawo ba" a cewar Dederi.
Saurari cikakken rahoto daga Baraka Bashir:
Your browser doesn’t support HTML5