Mahaifiyar Melanie Trump, matar tsohon Shugaban kasar Amurka Donald. Trump, Amalija Knavs, ta rasu, kamar yadda Trump ya tabbatar a wata sanarwa da aka wallafa a X, wanda a da ake kira Twitter. Amalija ta rasu tana da shekaru 78.
WASHINGTON, D. C. - Melanie ta rubuta a ranar 9 ga Janairu cewa "A cikin bakin ciki nake sanar da rasuwar mahaifiyata masoyiyata, Amalija," ta ce "Amalija Knavs mace ce mai kuzari wacce a ko yaushe ta ke kame kanta da mutunci, ta sadaukar da rayuwarta wajen kula da mijinta, 'ya'yanta, jikanta, da surukinta" wato Trump.
Ta ci gaba da cewa, "Za mu yi kewarta fiye da kima kuma za mu ci gaba da girmamata da kaunar gurbin da ta bari."
Har yanzu dai ba a tabbatar da musabbabin rasuwarta ba, ko da yake tsohon Shugaban kasa Donald Trump ya bayyana a wani taron da aka yi a Florida a farkon wannan watan cewa, surukar ta sa ba ta da lafiya sosai.