A Najeriya, yayin da aka shiga mako na uku da sace dalibai 39 na wata makarantar gaba da sakandare a jihar Kaduna, rahotanni na cewa mahaifin daya daga cikin daliban ya rasu sakamakon bugun zuciya.
Kawo yanzu dai babu tabbaci ko bugun zuciyar da Ibrahim Shamaki ya samu ya na da alaka da sace ‘yarsa, Fatima Shamaki wacce aka gani ta na magana a cikin wani bidiyo da ‘yan bindigar suka saki bayan wasu ‘yan kwanaki da sace su.
Karin bayani akan: Dalibai, jihar Kaduna, Nigeria, da Najeriya.
An tsinkayi wasu majiyoyi daga iyalan mamacin su na cewa Ibrahim Shamaki ya kamu da rashin lafiya bayan samun labarin sace ‘yarsa a ranar 12 ga watan Maris.
Gwamnatin jihar Kaduna na ci gaba da fuskantar matsin lamba daga iyayen daliban da sauran mutanen gari akan ta ceto daliban.
A cikin makon nan iyaye da wasu kungiyoyi sun yi ta zanga-zanga a kwalejin ilimin raya gandun daji ta tarayya da ke Kaduna inda aka sace daliban.
A ranar Juma’ar nan ne iyayen daliban suka gana da jami’an gwamnatin jihar Kaduna domin ganin gwamnatin ta kubutar da daliban.
Gwamnatin jihar dai ta sha jaddada matsayarta cewa ba za ta tattauna da ‘yan bindiga ba.
Yankin arewa maso yammacin Najeriya, ya shiga kanjin masu satar mutane don neman kudin fansa, lamarin da ya sa al'umomin da hukumomin da yankin ya shafa laluben hanyoyin da za su magance wannan matsala.
Wasu masu sharhi na ganin akwai bukatar gwamnatin ta bullo da hanyoyin da suka dace domin ganin an ceto daliban ba tare da wata matsala ba.