Makarantun kwana-kwanan da gwamnati ta bada umarnin a sake bude su, sun hada da Makarantar Gwamnati Ta Bai daya ta Unity dake Malumfashi, Kwalejin Karatun Arabiyya na addinin Musulunci na Sir Usman Nagogo wato SUNCAIS, Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Mata ta Jihar Katsina da ke Dutsinma, Makarantar Arabiyyar ta Gwamnatin Katsina ta Mata da ke Dutsinma, Makarantar Gwamnati ta Kurame da ke Malumfashi da kuma Makarantar Gwamnati ta Makafi ta Jihar Katsina.
Gwamnatin jihar Katsina ta kuma bada umarnin sake bude dukannin makarantun kwana na mata a asalin mazaunansu ko kuma makarantun da ke kusa da su daga ranar Laraba 24 ga watan nan na Maris.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Ilimin jihar, Badamasi Charanchi, ya rattaba wa hannu, inda Ma’aikatar Ilimin jihar ta jadada cewa, dole ne dalibai, malamai da baki da ke shiga da fita makarantar su rinka bin ka’idojin kula da lafiya da hukumomi suka gindaya na yaki da cutar corona.
Idan ba a manta ba, a ranar 28 ga watan Fabrairu ne gwamnatin jihar Katsina ta bada umarnin a sake bude wasu makarantun kwana 4 daga ranar biyu ga watan Maris.
wannan umarnin dai na zuwa ne kasa da wata 1 da komawa karatu na makarantun rana kafin gwamnati ta rufe makarantu har illa maa sha Allahu biyo bayan yin awun gaba da daliban makarantar sakandaren Kimiyar Gwamnati da ke garin Kankara 344 da ‘yan bindiga su ka yi a ranar 11 ga watan Disamban shekarar 2020.
A yayin fitar da sanarwar, Kwamishinan Ilimi, Badamasi Charanchi, ya yi karin haske kan cewa, makarantun kwana 4 ne za su koma bakin aikin koyarwa yadda su ka saba, wadanda suka hada da makarantun gwamnati dake Faskari da Musawa, Makarantar Gwamnatin Mata da ke Barkiya da kuma, Makarantar Sakandaren ‘Yan sanda da ke Mani.
Kwamishinan Ilimin jihar ya kara da cewa, ya kamata sauran daliban makarantun sakandaren 'yan maza, su koma karatu a makarantun sakandare da ke kusa da inda su ke zaune a yayin da takwarorinsu mata za su jira umarni daga gwamnati.
Jihar Katsina dai na da makarantun kwana 38, kamar yadda Kwamishinan Ilimin jihar ya bayyana.