Mahadi Kadai Zai Ture Sabbin Masarautun Jihar Kano-Ganduje

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya jaddada cewa, sabbin masarautu hudu da gwamnatinsa ta kafa za su ci gaba da zama na din-din-din.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin bikin ranar ma’aikata da aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, Kano a ranar Litinin daya ga watan Mayu, 2023.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta cece-ku-ce a kan gwamnatin Abba Yusuf mai jiran gado, inda wasu ke rade-radin cewa, mai yiwuwa sabuwar gwamnatin ta yi nazari a kan batun Masarautar Kano.

Hawan Fanisau (Facebook/ Masarautar Kano/ Kamfa Photography)

Rabiu Kwankwaso, dan takaran shugaban kasa na jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a zaben 2023, na daga cikin masu wannan ra’ayin kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo da ya fito.

Sai dai Gwamna Ganduje wanda ya raba masarautun Kano gida biyar sannan ya tsige Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na wancan lokacin, ya ci gaba da cewa, an samar da sabbin masarautun guda hudu ne da nufin kara samun hadin kai, da ci gaba da jin dadin al’umma. Ya kara da cewa an kirkiro masarautun ne domin girmama al’ummar yankunan da kuma dawo da martabar cibiyoyin gargajiya.

Lokacin da Tinubu ya kai ziyara fadar Sarkin Kano (Hoto: Muhd Photography Instagram, Kano Emirate)

Gwamna Ganduje ya kara jaddada cewa, sabbin masarautun sun kawo ci gaba a wadannan yankuna kuma za su kasance na dindindin.

“In Allah ya yarda sai Mahadi ka ture, kuma mahadin da zai ture Allah ba zai kawo shi ba”

A jawabin Gwamnan yace “Masarauta wata alama ce ta hadin kai, ci gaba, da jin dadin al’ummarmu. Ko da ba a gwamnati muke ba, muna addu’a kuma za mu ci gaba da addu’a Allah ya zaunar da wadannan,” inji shi.

Samar da sabbin masarautun dai ya kasance batun cece-kuce a Kano tun daga shekarar 2020, inda wasu ke goyon bayan matakin yayin da wasu ke adawa da shi.

Ku Duba Wannan Ma Gwamnan Jihar Kano Mai Jiran Gado Abba Yusuf, Zai Duba Batun Tsige Sarkin Kano Na 14, Muhammadu Sanusi - Kwankwaso

~Yusuf Aminu Yusuf~