Magoya Bayan Manchester United Zasuyi Zaman Dirshan A Gidan Zlatan

A jiya an buga wasa daya da yarage a kasar Ingila bangaren firimiya lig na bana mako na 26, Inda kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta lallasa Liverpool da kwallaye 3-1.

Leicester, ta samu nasarar jefa kwallonta ta farko a cikin minti 28, ta kafa dan wasanta mai suna Vardy, kwallo ta biyu kuwa ta kafar Drinkwater, a mintuna na 39, da fara wasan

Vardy, ya sake jefa kwallo a ragar Liverpool, a cikin minti na 60, bayan an dawo hutun rabin lokaci inda daga bisani Liverpool, ta rage kwallo daya a mintuna 68, ta kafar dan wasanta Coutinho, Haka aka tashi 3-1.

Wannan ya bada dama ga kungiyar Leicester, ta Fara dawowa da martabarta a matsayi na Goma sha biyar daga tsakiyar teburin da maki 24, a wasanni 26 da ta buga, ita kuma Liverpool, tana mataki na biyar da maki 49.

A ranar alhamis da ta gabata Leicester, ta sallami Mai horas da ‘yan wasanta Claudio Renieri, domin rashin tabuka abun kirki a bangaren Firimiyan bana.

Shi kuwa Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho, yace da yuwuwar magoya Bayan kungiyar ta Manchester zasuyi dafifi a kofar gidan Zlatan Ibrahimovic, domin ganin dan wasan ya amince ya kara tsawaita kwantirakin a Kungiyar.

Dan wasan mai shekaru 35, da haihuwa ya dawo kungiyar ta Manchester, a bana inda ya rattaba hanu na shekara daya tak a Kungiyar Inda a yanzu haka Zlatan, ya jefa kwallaye sama da ashirin a Manchester, sha biyar daga ciki duk a gasar firimiya ta bana

A ranar lahadi da ta wuce Zlatan, ya jefa kwallaye biyu a wasan karshe da sukayi da Southampton, na cin kofin EFL 2017 wanda haka ya bada dama ga Manchester United, ta lashe kofin a bana da kwallaye 3-2.

Manchester United, dai tana bukatar dan wasan ya kara tsawaita zamansa a kungiyar sai dai har yanzu dan wasan bai ce komi ba.