Kungiyar kwallon kafa ta Leicester City, dake kasar Ingila ta bada sanarwar Sallamar Mai horas da kungiyar Claudio Ranieri, a kan kujerarsa, hakan ya biyo Bayan rashin tabuka wani abin azo aganine da Kungiyar batayi a bana.
Ranieri, wanda yazo Kungiyar a shekara ta dubu biyu da Goma Sha Biyar kimanin shekaru Biyu kenan da suka wuce ya jagoranci Kungiyar ta Leicester City, har ta kai ga lashe kofin firimiya lig na kasar Ingila, a 2015/2016 bayan ta shafe shekaru sama da 100 da kafuwarta.
Wannan yasa hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta bashi gwarzon shekara a bangaren horaswa sai dai a Bana Kungiyar ta Leicester, ta kasa rike kambunta na firimiya domin a yanzu haka tana matsayi na Goma Sha bakwai ne da maki 21, a wasanni 25, da ta buga na firimiya.
A ranar laraba 22/2/2017, Leicester, ta sha kashi a hannun Sevilla, daci 2-1 a gasar cin kofin zakarun turai na bana a matakin wasan zagaye na sha shida, sai dai duk da haka tana da damar hayewa zagaye na gaba idan ta samu nasara jefa kwallo 1- 0 a wasan da zatayi da sevilla, karo na biyu a ranar 14/3/2017.
Hukumar gudanarwa na Leicester, ta nada mataimakin Claudio, mai suna Craig Shakespeare, a matsayin Mai horas da ‘yan wasan na rukon kwarya kafin ta zabi sabon kocinta.
Shakespeare zai fara wasansa na farko ranar litinin da kungiyar kwallon kafar Liverpool, a bangaren firimiya lig 2016/2017 mako na ashirin da shida.